Duk macen da takeyi maka daya dagacikin wadannan abubuwan to
tabbas takamu da sonka kuma duk yanda akai kunya ce ta hana ta fada ko tana
jiran kagane alamomin nan ne don kafara furtawa, kon watakila tsoran fada
takeji kace bakasonta karshe alakar da take tsakanin ka da ita ta lalace.
Ammafa ztz iya kasancewa kaima kana sonnata kuma kaima
tsoron fadar kake saboda haka, idan kuwa hakane daga yanzu baka da sauran
damuwa inhar tanama daya daga abubuwanbnan mun baka green light kaje kafesa
mata yanzu haka zakai mamakin murnar dazatai.
1.
Satar kallonka!
Muna satar kallon abu biyune kacal abun dayake matukar
burgemu da kuma abun dayake matukar bamu mamaki.
Kuma duk sanda kakama mai satar kallon ka zaka iyab gane
maiyima aciki sannan akwai wani abu dayake kayatarwa game da satar kallo shine,
dawuya kaga mace tana satar kallonka batare da kakama ta ba amma fa duk dahaka
bazaisa ta iya dainawa ba dalili kuwa shine zata iya boyewa zuciyarta amma fra
bazata iya boyewa idanuwanta abun begenta ba.
2.
Yin dariya!
Baban hanyar shiga jikin mutum shine sashi dariya da kuma
yin dariya akan abun dariyar sa, mata sunsan dahaka shiyasa duk namijin da suke
so suke kokarin sa shi dariya dakuma yin dariya akan abun dariyarsa ko da kuwa
baikai ai dariyarsa ba.
Misali sauda dama inkana zaune acikin mutane zaka zakai wani
abu dan kabawa mutane dariya saibayan kagama zaka fahimci abun bai bawa kowa
dariya ba hakan da kunya datakaice amma inda da macen datake boya sonka to tabbas
zakaga tayi dariya itama fa bawai abun yabata bane! Tayine kawai don kai tunanin
kasata dariya , idan akwai wadda takema hakan abokina akwai magana !
3.
Tambaya akan rayuwar soyayyarka!
Kamar irin cewa
·
Kanada budurwa ?
·
Ko yaushe zakai aure?
·
Ko wacce irin budurwa kafiso?
·
Yaushe zakayi aure?
·
Me yafi burgeka game da mata?
Ko kuma cewa aini namiji dogo nakeso idan kai dogone, kokuma
cewa aini bsaurayi megemu nakeso idan kanada gemu.
Tambayoyi irin wannan alamomine na tanasonka kuma tanason
sanin irin macen daka keso don tai kokarin zama irin ta.
4.
Kayi hakuri! Ko kahakura!
Macen da take yawean baka hakuri akan karamin abu wani
lokacin ma ba laifin ta bane amma still zakaga tana tacewa kayi hakuri abun
dayasa shine idan kana fushi abun dayake cikin zuciyarta sukarta yakeyi shiyasa
batadamu da laifinta bane konaka itadai batason taga ranka abace.
5.
Kawayenta sunsani!
Idan kana lura kawayenta zaka gane domin duk sanda ka wuce
ko kuma kahadu da su zakaga suna zungurar junan su dayin magana kasakasa ,
kakuma lura zakaga dukkaninsu ita suke kalla sannan sukuma kalleka sunsan
dalilin dayasa suke haka bayi inyi shiru basai na tona musu asiriba.
Abubuwa biyar din kenan…
